Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano ta Fitar da Ranar Zaɓen ƙananan Hukumomi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta ayyana 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.
Wannan ya zo ne bayan hukuncin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancinsu tare da umartar jihohi su samar da shugaban ƙaramar hukumar mai cikakken iko.
A baya-bayan nan ne gwamnatin Kano ta bayyana cewa a shirye take ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ba da daɗewa ba.
Read Also:
Da yake magana da ƴan jarida a Kano, shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ya ce hukumarsa a shirye take ta gudanar da zaɓen.
Malumfashi ya kuma ce za a yi wa duka ƴan takara gwajin shan miyagun ƙwayoyi kafin su cancanci tsaywa takarar.
A cewar shugaban hukumar, za a yi zaɓen fitar da gwani da mika muhimman takardun ƴan takara daga 6 ga watan Satumba zuwa 18 ga watan Oktoba.
Hukumar za ta saki sunayen ƴan takarar da suka cancanta a ranar 25 ga watan Oktoba.
Jam’iyyun siyasa kuma na da nan da 1 ga watan Nuwamba su sauya ƴan takara.
An gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na ƙarshe a jihar Kano ranar 16 ga watan Janairun 2021 a ƙananan hukumomi 44 da mazɓu 484.