Kano: Gobara ta Lashe Dakin Kwanan Kwalejin Horon Malaman Jinya

Akalla dakuna 16 a gidan daliban kwalegin horon malaman jinya da unguzoma ta jihar Kano sun kone kurmus sakamakon gobara.

An ce gobarar ta fara ci ne lokacin Sallar Magariba misalin karfe 6:20 a ranar Laraba a tsauni na uku da dakin kwanan Sa’idu Fagge.

An tattaro cewa wutan ta samo asali ne daga ban daki. Wata majiya a kwalejin ta bayyanawa The Punch cewa sai da aka kwashe awa daya ana gobararn kafin jami’an kwana-kwana suka iso. Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sa’idu Muhammad, ya tabbatar da aukuwan lamarin.

Ya ce an kaddamar da bincike domin gano abinda ya haddasa gobarar da kuma irin asarar dukiyan da akayi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here