‘Yan Jam’iyyar APC a Jahar Kano Sun Kafa Sabuwar ƙungiya mai suna APC Maslaha

Wasu ƴan jam’iyyar APC a jihar Kano dake arewacin Najeriya sun kafa wata sabuwar ƙungiya mai suna APC Maslaha, abin da ya kawo kashe-kashen jam’iyyar zuwa bangare uku.

Sabon ɓangaren dai na ƙarƙashin shugabancin Alhaji Aminu Dabo, wanda makusanci ne ga gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran jagororin ƙungiyar su ne Alhaji Kabiru Kama Kasa, da Alhaji Yusuf Ado Kibiya, da Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan Tama da farfesa Mukhtar Ɗankaka a matsayin Sakatare.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ɓangaren su Malam Ibrahim Shekaru suka yi watsi da tsarin da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta bi wajen kafa kwamitin da zai yi sulhu tsakaninsu da gwamna Ganduje, kan shugabancin jam’iyya a jihar.

Sai dai sabon ɓangaren na APC masalahar kamar yadda Babban Daraktan su Alhaji Yusuf Ado Kibiya ya shaidawa BBC su ba sa rigima da kowane ɓangare na jam’iyyar APC a Kano illa suna kokari ne su samar da daidaito a tsakanin ɓangarorin dake jayayya da juna a jihar.

A tattaunawarsa da BBC Alhaji Yusuf Kibiya yace sun fito ne domin sanya abubuwa a kan hanya da samun gyara a jam’iyyar ta APC.

“Duk abin da suke faruwa ba daɗi kowa ya gaji, kullum sai rigima, rigima, rigima,” a cewar Kibiya.

Yace sun fito ne ganin cewa kowa ya yi shiru, “to a irin wannan yanayi dole wasu su yi magana don a samu daidaito,” a cewar Kibya.

A cewarsa sun rubuta takardu ga manyan ɓangarorin dake rigima da juna, kuma suna sauraron su ji daga gare su.

To sai dai ɗaya daga jagoroin ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce fitowar wannan ɓangare tamkar wani wayo ne ake shirin a yi wa ƴan jam’iyyar, kasancewar shugaban APC maslaha ɗin suna tare da gwamna.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka kafa APC Maslaha sun yi haka ne da nufin sharewa kansu hanyar takara a zaɓukan 2023.

To sai dai Alhaji Yusuf Kibiya ya musanta cewa suna da wata manufa ta takara, inda yace babban fatansu shi ne a samu maslaha a jam’iyyar, a kuma magance matsalar rigingimu da jam’iyyar ke fama da su yanzu haka a jihar.

Amma a nasa ɓangaren, shugabancin jam’iyyar APC ɓangaren gwamna Ganduje ya ce ba shi da masaniya kan ɓangaren na APC Maslaha, don haka ba zai ce komai ba.

To sai dai Shugaban APCn ɓangaren Ganduje, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce suna zaune lafiya da mutanen da aka ce su ne shugabannin na APC maslaha, kuma babu wata matsala tsakaninsu.

Ra’ayin masana.
Fitowar wannan sabon ɓangare ko ƙungiya a cikin jam’iyyar APC a Kano ya ɗauki hankalin jama’a, inda wasu ke cewa jam’iyyar ta ƙara afkawa cikin wani rikicin na cikin gida.

To sai dai masana kamar su Malam Kabiru Sa’idu Sufi mai sharhi kan al’amuran siyasa na ganin ya yi wuri a yanke hukunci kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta APC Maslaha.

Ya ce amma abin da yake tabbas shi ne rikicin da ake fuskanta a APC ɗin ne ya haifar da ƙungiyar.

Malam Sufi ya ce dama a duk lokacin da zaɓuka suka ƙarato akan samu irin waɗannan ƙungiyoyi da suke fitowa da manufofi daban-daban na cimma buƙatar kai ko ta wasu.

Malamin wanda yake koyar da kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen jami’a ta jihar Kano ya ce “Za ta iya yiwuwa masu APC Maslahar sun ƙirƙire ta don samarwa kansu mafita da kuma cimma buƙatunsu.”

“Kuma zai iya yiwuwa wani ɓangare ne da suke rikicin APC a jihar ta Kano ya ƙirƙiri bangaren don cimma muradunsa,” inji Malam Sufi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here