Majalisar Dokokin Kano ta Amince Gwamna Abba ya Kafa Hukumar Tsaro Mallakin Jihar
Jihar Kano – Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin dokar da zai ba gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ikon kafa sabuwar hukumar tsaro.
Amincewar ta biyo bayan tattauna wa mai zurfi kan muhimman sassan kudirin, ciki har da sashen da ya haramta bai wa dan siyasa jagorancin hukumar.
Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Husaini Dala, ya bayyana cewa majalisar ta yi cikakken nazari kan kudirin don tabbatar da cewa dokar za ta amfanar da jihar Kano.
Dalilin majalisa na amince wa da kirkirar hukumar
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa bayan amincewar da aka yi da kudirin, Hon. Lawan Husaini, ya bayyana cewa an bi dukkan ka’idojin dokoki kafin majalisa ta amince da shi.
Dan majalisar ya bayyana cewa hukumar tsaron za ta kasance wani bangare na tsaron al’umma, wanda zai taimaka wajen karfafa aikin hukumomin tsaro a jihar.
Read Also:
Ya jaddada cewa kirkirar sabuwar hukumar za ta inganta tsaro a Kano, inda ya yi nuni da irin matakin da jihohin Kudu suka dauka na kafa hukumomin tsaro kamar Amotekun domin karfafa tsaro a yankunansu.
Hon. Husaini ya bayyana cewa hukumar za ta samu cikakken ikon rike makamai bisa doka, tare da ikon kama masu laifi da mika su ga ‘yan sanda domin gurfanarwa a kotu.
Majalisa: Sharuddan daukar ma’aikatan hukumar tsaro
Shugaban masu rinjaye na majalisar ya kuma bayyana cewa duk wanda za a dauka aiki a hukumar ba zai kasance ‘dan kowace jam’iyyar siyasa ba.
Hon. Dala ya ce:
“A cewar dokar, shugabancin hukumar zai kasance a hannun wani dan asalin jihar Kano wanda ba shi da wata alaka da kowace jam’iyyar siyasa.”
Majalisa ta fadi sharadin zabar shugaban hukumar tsaro
Hon. Lawan Husaini Dala ya kara da cewa za a nada Kwamanda Janar na hukumar, wanda dole ne ya zama mutumin kirki mai kima da kwazo, sannan kowace karamar hukuma za ta nada kwamanda.
Ya ce dole Kwamanda Janar din ya zama tsohon jami’in soja ko ‘yan sanda da ya shafe akalla shekaru 25 yana aiki, kuma ba zai kasance a ƙasa da mukamin Kanal a soja ko Kwamishinan ‘yan sanda ba.
Hon. Dala ya kara da cewa hukumar tsaron za ta samu kwamitin gudanarwa da za a dora wa alhakin tafiyar da ita, tare da shugaban da gwamna zai nada.