Gwamnatin Kano Zata Dauki Matakai 6 Kan Zanga-Zanga

 

Kano – Gwamnatin jihar Kano ta ce ta nuna takaicinta kan yadda wasu yan daba suka kwace zanga-zangar lumana suka mayar da ita ta ta’addanci.

Gwamnatin ta ce tana da cikakken rahoto kan yadda zanga-zangar ta jawo asarar rayuka, lalata dukiya, sace kayan jama’a da dai sauran su.

Gwamnatin Kano ta magantu kan zanga-zanga Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf ya fitar, wadda Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa a shafinsa na X.

Sanarwar ta ruwaito Gwamna Abba Yusuf yana nuna takaicinsa kan yadda wasu ‘yan siyasa marasa kishi’ suka kuduri aniyar haddasa rikici a Kano domin manufarsu ta siyasa.

Gwamnan ya tabbatar da cewa za a hukunta duk wanda aka kama da tayar da zaune tsaye a jihar yayin da yake ci gaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa, a cewar sanarwar.

Gwamnatin Kano ta dauki matakai 6

Sai dai duk da hakan, sanarwar ta ce gwamnati ta dauki wasu matakai da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarta, wadanda take son jama’a su mayar da hankali kansu.

1. Hukunta masu tayar da zaune tsaye

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da hukunta sama da mutane 600 da aka kama bisa zargin sun tayar da zaune tsaye a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar.

An ce za a fara hukunta wadanda ake zargin ne daga yau Litinin, 5 ga watan Agustan 2024.

2. Za a bude cibiyoyin horas da matasa

Gwamnan Kano ya ba da umarnin dawo da koyarwa a cibiyoyin horas da matasa sana’o’in dogaro da kansu, inda za a yiwa dubunnan matasa rijista domin su zamo masu dogaro da kansu.

3. Cibiyar gyaran tarbiya za ta fara aiki

Cibiyar gyaran tarbiya ta Kano da ke Kiru ta za ta fara horar da matasan da ke fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi nan da wani lokaci.

4. An kafa kwamitin binciken zanga-zanga

Gwamna Abba Yusuf zai kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai binciki kashe-kashe da barnata kadarori na gwamnati da na jama’a da aja yi a jihar Kano.

Sanarwar ta ce gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun kiraye-kiraye daga ‘yan Najeriya, kasashen ketare, kungiyoyin kare ‘yancin dan Adam, sarakuna da malamai.

5. Neman hadin kan al’ummar Kano

Gwamnati ta yi kira ga mutanen Kano da su goyi bayan wadannan matakai ta hanyar samar da bayanai masu amfani ga kwamitin binciken wanda za a kafa nan gaba kadan.

6. Gwamnati ta magantu kan daga turar

Rasha A karshe, sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Yusuf ba ta da alaka kai tsaye ko ta fakaice da duk wasu masu zanga-zanga musamman masu daga tutar wata kasar waje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here