Kano Waje ne Mai Matukar Muhimmanci Domin Nan ne Gidan Masu Akida ta Ci Gaban Kasa – Osinbajo

 

Mataimakin shugaban kasa ya nemi masu kira ga wargajewar kasar da su sake tunani.

Osinbajo yayi wannan kiran yayin gabatar da jawabin sa a taron tattaunawa na 12 na Bola Tinubu.

Hakazalika Osinbajo ya yabawa jihar Kano saboda kasancewarta gida ga masu son cigaba.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu kira ga raba Najeriya da su sake tunani, ya kara da cewa idan Najeriya ta wargaje, dole su bukaci katin biza domin tafiya sassan arewa kamar Kano.

Osinbajo ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron tattaunawa na 12 na bikin cika shekaru 69 na Bola Tinubu da aka gudanar a jahar Kano, jaridar Punch ta ruwaito.

Mataimakin Shugaban kasar, wanda shine babban bako na musamman, ya ce taron a farko an shirya gudanar dashi ne ta yanar gizo, amma Gwamna Abdullahi Ganduje na Jahar Kano ya dauki nauyin taron a zahiri wanda kuma zai gudana ta manhajar Zoom.

“Ga masu son ballewa zuwa kananan abubuwa, zuwa kananan kasashe, ya kamata a tuna musu cewa da ba za mu iya karbar tayin Gwamna Ganduje na zuwa Kano a takaitaccen lokaci ba tunda duk da za mu bukaci Visa don zuwa Kano,” in ji Osinbajo.

Osinbajo ya kara da cewa Kano waje ne mai matukar muhimmanci domin nan ne gidan masu akida ta ci gaban kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here