Majalisar Kano ta Soki Tsarin Rusau da ya yi Sanadin Mutuwar Mutane 4

 

Jihar Kano – Majalisar dokokin jihar Kano ta yi Allah wadai da kalaman shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu ya yi a kan aikin rusau a Rimin zakara da ya kashe mutane hudu.

A zaman majalisar na ranar Laraba, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo a zauren, Aminu Sa’adu Ungogo ya bayyana cewa yadda aka dauko aikin rusau din bai dace ba.

A wani bidiyo da Hon Musayyib Kawu Ungogo ya wallafa a shafin Facebook, an yadda yadda dan majalisar ya nanata cewa rai ba abin wasa ba ne, saboda haka dole a zurfafa bincike a kan lamarin.

Ya zargi Shugaban jami’ar Bayero da cewa bai cancanci matsayin da ya ke rike da shi ba, duba da yadda ya ke kalaman da ke kaskantar da ran dan adam.

Majalisar Kano ta soki tsarin rusau

Dan majalisar Ungogo a majalisar dokokin Kano ya bayyana cewa babu inda za a amince da a shiga gidajen jama’a da talatainin dare domin gudanar da rusau.

Hon Aminu Sa’adu Ungogo ya ce:

“Ashe ba a sani ba, wasu jami’ai ne su ka je, su ka yi wannan aiki, sakamakon haka aka rasa ran mutum hudu,.”

“Wasu daga cikinsu, aka ji masu raunuka, har da harbe-harbe, wanda wasu daga ciki yanzu su na nan, a asibiti a kwance ana kula wa da lafiyarsu.”

Ya kara da cewa wannan lamari da ya afku abin kaico ne, abin takaici ne, kuma abin Allah wadarai ne.

Majalisa za ta dauki mataki a kan rusau

Hon. Aminu Sa’adu Ungogo ya mika bukatarsa ga majalisar dokokin Kano a kan matakan da za a dauka domin mutunta ran dan adam da tabbatar an yi mutanen Rimin Zakara adalci.

Ya ce: ”

Lallai a yi kwamiti a gidan nan wanda zai bincika, kuma ya tabbatar da irin abin da ke wakana, kuma ayi hukunci na gaske a kan wadanda aka zalunta aka kashe su ba-su-ji-ba ba-su-gani-ba a cikin talatainin dare, domin ya saba ka’ida.

“Na biyu, lallai ne a samarwa da wadanda su ka jikkata da wadanda su ka rasa iyalansu madogara a cikin rayuwarsu, yadda za su ci gaba da yin rayuwa cikin sauki, ba da aka kuntata masu.

Dan majalisar ya kuma shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf, a kan ya tabbatar an dauki mataki a kan duk wanda aka kama da laifi a rusau da ya gudana a Rimin Zakara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here