Dalilin da Yasa Gwamnatin Kano Zata Sauyawa Gidan Zoo Mazauna
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta sauya matsugunin gidan ajiyar dabbobin jeji daga cikin birni zuwa gefe guda.
A cewar gwamnan jihar Kano, Dakya Abdullahi Umar Ganduje, dabbobin jeji basa son hayaniyar mutane.
Ibrahim Ahmad, kwmishinan al’adu da harkokin bude ido, ya ce bayan sauya matsugunin, za’a inganta sabon wurin da za’a koma.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin a sauya wa gidan ajiye naman jeji (gidan Zoo) matsuguni daga cikin birni saboda matsarsa da jama’a suka yi.
Kwamishinan Al’adu da harkokin buɗe ido, Ibrahim Ahmad, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce dabbobin, yanzu, a takure su ke a matsunguninsu saboda ko kadan basa son hayaniyar mutane.
Read Also:
Da yake magana da gidan Rediyon Freedom, kwamishinan ya ce za’a sauya matsugin dabbobin zuwa garin Tiga da ke yankin ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano.
Ya ce; “mu na aiki a kan yadda za’a sauya matsugunin gidan zoo saboda al-umma sun kewaye inda yake wanda hakan ke takurawa dabbobin. Da yawa daga cikin dabbobin basa son hayaniya sosai.
“Saboda haka zamu sauya matsugunin gidan ajiye dabbobin, sannan mu ƙara masa matsayi daidai da zamani, yadda jama’a daga wurare daban daban zasu yi marmarin ziyartarsa”.
A cikin watan Oktoba na shekarar 2019 ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa wani zaki da ya tubure a gidan Zoo na Kano ya yi kutse zuwa kejin adana Jimina, inda ya cinye guda daga cikinsu.
Daga bisani masu kula da dabbobin da ke gidan ‘Zoo’ din sun yaudari Zakin da wasu Akuyoyi biyu domin ya fito daga kejin adana Jiminonin gidan.
Sa’idu Gwarzo, shugaba a gidan Zoo na Kano ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa an samu Zakin ne a cikin farfajiyar kejin da aka saka Akuyoyi bayan ya cinyesu gaba daya.