Gwamnan Kano ya Umarci Masarautun Jihar Guda 4 da su Shirya Hawan Sallah
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya umarci masarautun jihar guda hudu da su shirya gudanar da hawan Sallah karama a bana.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a lokacin taron buda baki na Ramadan da aka yi tare da Sarakuna a Ante Chamber, Fadar Gwamnatin Kano, a ranar Talata.
A sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa hawan sallar na da muhimmanci, musamman wajen nishadantar da jama’a.
Gwamna Abba ya fadi muhimmancin hawan sallah
Gwamna Abba ya ce jama’ar jihar na matukar sa ran ganin bikin Sallah, inda suke sanya sababbin kaya, suna cika tituna domin kallon Sarakunansu a kan doki, tare da sada zumunci.
Saboda haka, Gwamnan ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ba za a hana jama’a wannan hakki nasu ba.
Read Also:
Ya tabbatar da cewa dukkan hukumomin tsaro na jihar za su kasance cikin shiri domin samar da cikakken tsaro ga jama’a yayin hawan bukukuwan sallah.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da majalisar masarautar Kano a watan Afrilu na wannan shekara domin ta fara aiki yadda ya kamata.
Har ila yau, ya ce za a bayyana ka’idoji, dokoki da sauran muhimman abubuwa da suka shafi majalisar a ranar da za a kaddamar da ita.
Gwamna Abba ya jinjinawa sarakunan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa sarakunan Kano bisa kwarewa da dangantaka mai kyau da suka nuna tun bayan nadinsu.
Ya na ganin wannan ne karon farko a tarihin jihar da aka samu irin wannan girmamawa tsakanin sarakunan, musamman dangane da tsarin matsayi da daraja a masarautun.
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da sauran sarakunan masarautun masu daraja ta biyu.
Ya kuma roki Gwamnan Kano da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya domin yada manufofi da shirye-shiryen gwamnati zuwa ga jama’a, domin tabbatar da aiwatar da su cikin sauki da inganci.