Kano Itace Jahar da Tafi Yaki da Cin Hanci da Rashawa – Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje ya jinjinawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Ganduje ya ce hukumar ta jihar ta fi kowacce tasiri da karfi a Najeriya.
A cewar gwamnan, wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar sun rasa aikinsu saboda aikin hukumar ta yaki da rashawa.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, ita ce mafi karfi a kasar nan wajen inganta lissafin kudaden jama’a da kuma jagoranci nagari.
Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na kungiyar akawun Najeriya (ANAN) wanda aka gudanar a Nassarawa GRA, Kano, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.
Read Also:
“A Kano muna da hukumar yaki da cin hanci mafi tasiri.
Sakamakon aikin hukumarmu ta yaki da cin hanci da rashawa, wasu kwamishinoni sun rasa ayyukansu.
Haka ma wasu sakatarorin din-din-din da daraktan ma’aikatar gwamnatin jihar suka rasa ayyukansu.
“Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da sauran hukumomin yaki da rashawa ta tarayya ne suka horar da ma’aikatan hukumarmu ta yaki da rashawa. Saboda su samu gogewa ta zamani wajen yaki da rashawa,” in ji shi.
Gwamnan ya yaba ma kungiyar akawun, cewa aikinsu mai rai ne sannan ya bukace su da su ci gaba da hada kansu da karfafa kansu, Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A nashi jawabin, Shugaban kungiyar, Farfesa Muhammad Akaro Mainoma ya yi godiya ga gwamna Ganduje a kan inganta Kano da yayi.