Kano: Gwamnatin ta Kafa Kwamiti Don Zaftarewa Iyaye Kuɗin Makaranta
Gwammatin jihar Kano ta sanar da kafa wani kwamiti da zummar aiwatar da shirin zaftarewa iyayen ɗalibai a jihar kuɗin makaranta da kashi 25 cikin 100 sakamakon gararin da annobar korona ta jefa mutane a ciki.
Kwamishinan ilimi na jihar Muhamad Sanusi Sa;idu Ƙiru ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Read Also:
Kwanan baya ne aka fara samun rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da masu makarantu masu zaman kansu, saboda buƙatar gwamnati ta ganin an ragewa iyaye kuɗin makarantar saboda annobar korona.
Su dai masu makarantun na cewa suma annobar ta shafe su, sannan basu da wata hanya ta biyan malaman da ke koyarwa albashinsu idan suka aiwatar da buƙatar gwamnatin.
Sai dai kwamishinan ilimi na jihar ya ce makarantu masu zaman kansu da dama a jihar sun fara aiwatar da sabon tsarin.