Ta’addanci: Lauyoyin Nnamdi Kanu sun Buƙaci Gwamnati ta Janye Zargin da Take Masa
Lauyoyin Nnamdi Kanu, jagoran ƴan awaren Biyafara, sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta janye zargin ta’addanci da ake masa, ko kuma a bayar da shi beli domin ya samu isasshen lokacin shirya kare kansa.
Lauyoyin sun bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, inda suka ƙara da cewa wanda suke karewa yana tsare ne a wajen hukumar DSS.
Read Also:
Aloy Ejimakor, shi ne jagoran lauyoyin na Kanu, ya ce, “Inda ake cigaba da tsare shi a ofishin DSS ba shi da kyau sosai, kuma ba zai samu natsuwar shiryawa domin kare kansa a kotu ba a wajen.”
Lauyan ya ƙara cewa dalilin da ya sa Kanu ya buƙaci wancan mai shari’ar da ke sauraron shari’ar ta janye shi ne tunanin da yake cewa ana tauye masa haƙƙinsa na ɗan Adam, kuma ba a ba shi damar kare kansa.
Shi ma barista Nnaemeka Ejiofor, ya ce abin da Kanu yake buƙata a yi masa ba raina kotu ba ne, illa kawai yana amfani da damar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada masa.
Shi ma wani daga cikin lauyoyin nasa, Jude Uguwanyi ya alaƙanta cigaba da fama da matsalar tsaro da ake yi a kudu maso gabas da cigaba da tsare Kanu da gwamnati ke yi.