Gwamnatin Najeriya ta ƙara Kashi 50 na Kuɗin Abincin Fursunoni da ke Faɗin ƙasar
Gwamnatin Najeriya ta amince da ƙara kashi 50 na kuɗin abincin fursunonin da ke gidajen gyaran hali a faɗin ƙasar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja babban birnin ƙasar, kakakin Hukumar Gidajen Gyara Hali na ƙasar, Umar Abubakar ya ce an ƙara kuɗin abincinne la’akari da yanayin tsadar abinci da ake ciki.
Ya ce ƙarin zai fara aiki ne daga watan Agusta a wani yunƙuri na inganta rayuwar mazauna gidajen yarin.
Read Also:
“Kwana huɗu da suka gabata na yi wa tattaunawa a game da wani bidiyo da ake yaɗawa da ake zargin na abincin ƴan gidan yari ne. Tuni Hukumar Gidajen Gyara Hali ta kafa kwamitin bincike a kan bidiyon, sai dai ba zan yi magana sosai a kan sakamakon binciken ba.
“Amma saboda tsadar abinci, Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙara kuɗin abincin ƴan gidan yari da kashi 50, kuma wannan karo na farko na ƙarin ne”.
Ya kuma bayyana cewa mazauna gidajen yarin da dama suna karatu a jami’o’in Najeriya, a cewarsa har da mutum shida masu karatun PhD, da kuma mutum 1,000 masu karatun digiri na farko a lokacin da suke zaune a gidajen yarin.