Gwamnatin Tarayya ta Kara Farashin Wutar Lantarki

Bayan karin farashin wuta da akayi a Nuwambar 2020, an sake tafka wani karin.

Hukumar NERC ta ce nan da Yunin 2021 za ta kara wani karin kuma.

Yan Najeriya basu gama kokawa kan karin baya ba gashi an samu sabon kari.

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta amince da kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastomomi ke biya yanzu a fadin tarayya, rahoto daga Daily Trust.

Hakan zai shafi kamfanonin raba wutan lantarki 11 dake Najeriya.

Wannan na zuwa ne watanni biyu kacal da kara farashin a watan Nuwamba 2020.

A cewar umurnin waiwayan farashin shekara-shekara da sabon shugaban NERC, Engr. Sanusi Garba, ya rattaba hannu ranar 30 ga Disamba, 2020, kuma aka gani ranar Talata, an fara dabbaka sabon farashin ne fari daga ranar 1 ga Junairu, 2021.

A umurnin mai lamba NERC/225/2020, ta bayyana abubuwan da tayi la’akari da su wajen kara wannan farashi.

A cewar ta, anyi la’akari ne da hauhawar tattalin arzikin 14.9% da akayi a Nuwamba, 2020, da kuma tashin dalar Amurka zuwa N379.4/$1 a karshen Disamba, 2020.

Hakazalika an lura da adadin wutan da aka samu tatsowa, hauhawar tattalin arzikin Amurka na 1.2% da kuma kudin da kamfanonin wutan lantarki zasu yi amfani wajen inganta wutan lantarki .

Wannan sabon farashin zai shafi kowa da kowa sabanin na baya da ya togaciye wadanda basu samun wutan lantarki sama da awanni 6 a rana.

Wannan farashin zai kasance daga yanzu zuwa Yunin 2021, kafin kuma aka sake karawa daga Yuni zuwa Disamba 2021, NERC ta bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here