Wanda Suka Kara Kawo Matsalar Rashin Tsaro – Sanata Ita Enang
Ita Enang ya zargi Gwamnonin Neja-Delta da azalzala wutar rikicin yankin.
Sanata Enang yace Gwamnonin Jihohi suka sa ake samun rikici a Neja-Delta.
Hadimin Shugaban kasar yace al’ummar ba su amfana da karin kason 13%.
Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin Neja-Delta, Ita Enang, ya yi magana game da harkar rashin tsaro.
Sanata Ita Enang ya zargi gwamnonin jihohin yankin Neja-Delta da kasa a gwiwa wajen samar da tsaro.
A yau ne jaridar Daily Trust ta rahoto hadimin shugaban kasar yana zargin gwamnonin jihohi masu arzikin fetur da rashin kawo zaman lafiya.
Read Also:
Sanata Enang ya bayyana haka ne yayin da kungiyar DROAN ta masu matatar danyen mai a Najeriya suka kai masa wata ziyara a ofishinsa.
Enang ya ce: “Gwamnonin sun yi sanadiyyar da yankunan da ke da danyen mai ba za su zaunu ba,” Ya ce a dalilin haka ake da matsalar rashin tsaro.
Da yake jawabi a gaban ‘ya ‘yan kungiyar DROAN, Enang ya ce karin kason kudin da ake ba yankin sam bai yi amfani wajen kawo cigaba ba.
Ya ce: “Gwamnonin bangaren Neja-Delta sun kawo matsalar rashin tsaro saboda kin amfani da kason 13% wajen kawowa yankunansu cigaba.”
A dokar kasa, ana ware karin kudi na musamman wajen rabon kason FAAC, wanda ake ba duk wata jiha da ta ke da arzikin man fetur a Najeriya.
Mai ba shugaban kasa shawara, Ita Enang, ya taba rike kujerar Sanata a Akwa Ibom, jihar da ta fi kowace arzikin mai a kasa, kafin ya koma APC.