Matsalar Karancin Abinci Mai Gina Jiki ga Yara ya ƙaru da Kashi 160 a Arewacin Najeriya
Wata kungiya mai zaman kanta, FHI 360, ta yi gargadi game da karuwar matsalar karancin abinci a tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekara biyar a arewa maso gabashin Najeriya.
Ta ba da rahoton cewa an samu tashin hankali sosai, inda yara 15,781 ke fama da rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Fabrairu da Satumba, wanda ya nuna kusan karuwar kashi 160 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Read Also:
An bayyana lamarin a matsayin mai tsanani, kuma ana bukatar karin tallafi cikin gaggawa don magance matsalolin lafiya da abinci mai gina jiki, musamman ga mata da yara a yankin.
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu a duniya wajen fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki musamman a yankin arewacin ƙasar.
Yayin da kimanin yara miliyan biyu a Najeriya ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, kashi 20 cikin 100 ne kawai ke karɓar magani.
Bayanai daga UNICEF sun kuma nuna cewa rashin abinci mai gina jiki na da matukar tasiri ga kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara a Najeriya a tsakanin ‘yan kasa da shekaru biyar.