Babban Lauya ya yi Kira da a Kara wa Shugaba Buhari Wa’adin Mulki

Babban Lauya, kuma dattijon kasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023, Daily Trust ta rawaito.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.

Ya ce ba daidai ba ne a yi imani cewa Shugaban kasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki biyu ba.

Clarke ya ce shugaban kasar na iya kara wa kansa wa’adin watanni shida domin gudanar da zabe cikin lumana.

Cikakken bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here