Hukumar Kare Hakki Bil Adama na Bincike Kan zargin kisa a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Kano
Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da haɗin gwiwar kungiyoyin farar-hula a Kano sun kaddamar da kwamitin bincike kan zargin kisan mutane uku a zaɓen fidda gwanin da APC ta gudanar a Kano.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito yadda wani mai takarar gwamna a inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya zargi cewa an kashe magoya bayansa da jikkata da dama a lokacin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar ranar Alhamis.
Read Also:
Kwamitin mutane 11 da aka naɗa karkashin jagoranci, Shehu Abdullahi na hukumar kare hakkin bil’adama da Ibrahim Waiya na ƙungiyar farar-hula a Kano.
Waiya ya ce ana saran kwaimitin ya gabatar da rahoton da ya tattara nan da mako uku domin gaggauta bincike.
Sannan an samu wata gamayar kungiyoyin farar-hula a Kano da su ma suka bukaci a soke zaɓen fitar da gwani na APC kan zargin tafka kura-kurai da aringizo.
Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne dai ya lashe zaɓen bayan doke abokin takararsa Sha’aban Ibrahim Sharada.