Tony Ojukwu ya Shawarci Gwamnatin Najeriya Kan Kare Makarantu Daga Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta kasa Tony Ojukwu ya shawarci gwamnatin Najeriya kan kare makarantu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a Abuja a wani taron kasa da kasa na hudu domin tabbatar da tsaron makarantu a kasar.

Ya ce hare hare kan makarantu da musamman kisa da sace dalibai, zai haifar da mummunan tasiri ga lamuran karatu a kasar.

Ya ce za a yi irin wannan taron a karon farko a Najeriya, wanda zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da yadda ta shafi ilimi a kuma tattauna kan hanyoyin tsaron da za a inganta ilimi a Najeriya ga yara masu tasowa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here