Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya Ƙarfafa Gwiwar Dakarun sa Domin Magance Rashin Tsaro
Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya yi kira ga dakarun rundunar da su cigaba da jajircewa domin tabbatar da cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga sun miƙa wuya.
Babban hafsan ya yi wannan kira ne a yayin kai ziyarar aiki Birged ta 23 da ke Yola ranar 27 Nuwamba 2021, inda ya saurari bayanai akan ayyukan rundunar daga Kwamandan ta, Birgediya Janar Aminu Garba.
Read Also:
A jawabin sa ga dakarun rundunar Birged ta 23 a Barikin Gibson Jalo, Babban hafsan ya tabbatar da magance matsalolin su domin gudanar da ayyukan su ba tare da mishkila ba.
Babban hafsan ya bayyana buƙatar cigaba da horon dakarun domin kyautata ƙwarewar su wajen magance ƴan ta’adda.
A yayin ziyarar, Babban hafsan ya ƙaddamar da rukunan gidajen dakarun biyu wadda ya dace da manufar sa na kyautata walwalar dakarun. Babban hafsan ya yi kira a gare su da su yi kyakkyawan amfani da gidajen don jin daɗi da walwalar su.
Birgediya Janar Onyema Nwachukwu
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojojin Kasan Najeriya
27 Nuwamba 2021