Fadar Shugaban Kasa Tayi Karin Haske Kan Ziyarar da Shugaba Buhari ya Kai wa Tinubu a Landan

 

Femi Adesina ya yi karin bayani kan ziyarar da Muhammadu Buhari ya kai wa Bola Tinubu.

Fadar Shugaban kasa tace ziyarar ban-girma ne kawai Buhari ya kai wa Jigon na APC a gida.

Hadimin Shugaban Najeriyan yace Buhari ba zai yi garajen goyon bayan wani ‘dan siyasa ba.

Abuja – Babban hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya yi karin haske game da ziyarar da Muhammadu Buhari ya ka kai wa Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ce mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari wajen harkar yada labarai da hulda jama’a ya ce ziyarar ba ta da alaka da siyasar 2023.

Femi Adesina yake cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya kai wa Bola Tinubu ziyara a Landan ne domin ya gaida shi saboda ana rade-radin bai da lafiya.

Hadimin shugaban Najeriyar ya yi karin hasken ne da ya bayyana a wani shiri na siyasa, Politics Today da gidan talabijin nan na Channels ta saba shirya wa.

“Kwarai kuwa, ta tabbata ya kai masa ziyara, amma ziyarar barka ce kurum da fatan alheri.”

“Mun san Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan kusan tun lokacin da shugaban kasa yake can, ba mu yarda da abin da muka karanta a kafofin zamani ba.”

“Amma mun ta jin labari game da rashin lafiyar Asiwaju Tinubu, saboda haka shugaban kasa ya kai masa ziyara ne saboda kauna.

Babu alakar ziyarar da 2023

Game da burbushin siyasa a wannan ziyara, Adesina yace lokaci bai yi ba da za a soma yakin neman zaben shugaban kasa, akwai sauran lokaci tukuna.

“Shugaban kasa ya na da ragowar shekaru biyu babu watanni uku a wa’adinsa. Saboda ba zai tada fara kamfe ba, shugaba Buhari ba zai taba yin wannan ba.”

“Kafin zaben 2019, mutane suka fara yi masa (Buhari) kamfe kafin hukumar INEC ta buga gangar siyasa. Shi ya fito ya ce ‘a daina garajen yakin neman zabe.”

“Saboda haka shugaban kasa da kan shi ba zai fito yana goyon bayan wani ‘dan takara yanzu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here