Karin Harajin VAT Zai Jefa Talaka Cikin Mawuyacin Hali – Atiku

 

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce karin harajin VAT da ake shirin yi a kasar nan zai zama wata wuta da za ta cinye rayuwar al’ummar Najeriya.

Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu tare da masu ba shi shawara, sun yanke shawarar kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10%, duk da sanin cewa NNPCL ya kara kudin man fetur.

Atiku na adawa da karin haraji

Dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023 a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, ya ce matakin ya bayyana wani sabon tsari na azabtar da ‘yan kasar.

A cewarsa, kara harajin zai ruruta matsalar tsadar rayuwa a cikin kasar da kuma kara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin Najeriya da tuni ya samu matsala.

Atiku ya yi ikirarin cewa Tinubu da mukarrabansa sun koma amfani da dabararsu ta jefa talaka a cikin mawuyacin hali yayin da a hannu daya suke almubazzaranci da dukiya.

Atiku ya ba Tinubu shawara A cewar jagoran na PDP, Tinubu bai damu da halin da talakan kasar ke ciki ba, sai dai ya fi damuwa da mallakar jiragen sama da gyaran manyan gidaje domin amfaninsa da iyalansa.

Atiku ya ce:

“Kara haraji ya jawo kamfanoni da ‘yan kasuwa da dama rugujewa wanda ya jawo rasa ayyukan mutane da kuma karin wahalhalu ga ‘yan talakan kasar.

“Masa’antar kere-kere ta kasance cikin mawuyacin hali tun hawan Tinubu. Haka zalika, tunda gwamnati mai ci ta waiwayi harkar noma, komai a bangaren ya tabarbare.”

Atiku ya ba Tinubu shawarar cewa su karkatar da tsare tsarensu kan abubuwan da za su kawo sauki ga ‘yan kasar da kuma gyara tattalin arziki maimakon abin da zai jawo tabarbarewarsu

Tinubu na shirin kara haraji

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce tana shirin kara haraji na kimar kayayyaki (VAT) daga 7.5% da ake caja yanzu zuwa 10%.

aiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji, ya ce kwamitin zai gabatar da wata dokar karin harajin ga majalisar dokoki.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here