Farfesa Umar Labdo Muhammad mutumin da yayi kaurin suna wajen sukar manufofin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya wallafa wannan bayanin a shafinsa na Facebook inda yake kira ga Sarkin Kano da ya daina surutu ya kama aiki.

“Wannan magana gaskiya ce; Nijeriya muna fama da talauci. Amma me shugabanni irin su mai martaba suke yi domin magance matsalar? Mai martaba masani ne gogagge a fannin tattalin arziki kuma hamshakin attajiri mai abin hannu. Wace gudunmawa ta kashin kansa ya bayar don rage talauci a tsakanin al’ummarmu. Ni dai a sanina babu wata makaranta, masana’anta ko irin kungiyoyin nan na taimako da ake kira NGO da mai martaba ya kafa don taimakon mutane, tare da cewa Allah ya yi masa baiwa da muka ambata a sama ta ilmi da kudi kuma ga sarauta.

Dalili ke sa a fadi magana. Na kan ji kunya da abinda Turawa suke cewa “disappointment” duk sa’ad da na wuce ta Kofar Kudu na ga mata sun yi cincirindo suna karbar sadakar taliya sinki daya (ba kwali guda ba). Ni da a zatona, kasancewar sabon sarkinmu dan zamani ne, mai ilmi, mai wayewa, mai “connection” a gida da kasashen waje, kuma ga shi kicima, ya ja kaya, zai jefar da waccan tsohuwar hanya ta taimakon mutane da abincin da ba zai ishe su ci daya ba.

Na yi tsammanin mai martaba zai fito da wani shiri mai dogon zango na fitar da al’ummarsa daga kangin talauci, ba kurum magana ta fatar baki ba. Shekara hudu da darewa karagar mulkin Kano ya kamata a ce mutane sun fara gani a kas.

Me Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II yake shirin bari don a tuna shi bayan mutuwarsa kuma ya iske a cikin kabarinsa? Ina masu ba sarkin shawara? Suna ba shi shawara ta kwarai ko kuwa fadanci kawai suke yi da kirari?

Mu a nan muna ba shi shawara da ya dubi matsayinsa a tarihi kuma ya gode baiwar da Allah ya yi masa ta hanyar yiwa mutanensa hidima da aiki, ba da magana kawai ba.
A ganinmu, mai martaba ya yi magana da yawa. Yanzu saura aiki.”

The post Karuwar Talauci: Aiki ya kamata Sarkin Kano ya yi ba surutu ba – Farfesa Labdo appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here