Ƙasashen da Suka Hana Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Zaman Lafiya – Touadéra
Shugaban ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya zargi ƙasashen yamma da hana ƙasarsa zaman lafiya da gangan, kwanaki kaɗan bayan ganawarsa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron.
Read Also:
Shugaba Touadéra ya ce ƙasar ta fuskanci wahalhalu daban-daban tun samun yancin kai kama daga satar kuɗin ƙasar da ƙasashen yamma suka yi sanadiyar rashin tsayayyar gwamnati ko kuma amfani da kamfanoninsu wajen taimaka wa kungiyoyin ta da ƙayar-baya wanda yawancin jagororinsu suka ƙasance daga waje.
An zargi dakarun ƙasar da wasu sojojin haya na kungiyar Wagner daga Rasha da ta ke hakkin ɗan adam, wanda ya janyo Tarayyar Turai ta saka wa wasu manyan jami’an kungiyar takunkumi.
A taron MDD da ake gudanarwa a Qatar, shugaban ya ce ƙasashen yamma sun mayar da ƙasarsa wurin tasa na albarkatun ƙasa, inda ya ce hakan ya sanya ƙasar da kuma wasu rashin dogaro da kai da kuma samun zaman lafiya mai ɗorewa.