‘Yan Kasashen Ketare da Dama Sun Nuna Sha’awar Son Zama ‘Yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa fiye da mutum dubu talatin da takwas sun nuna sha’awar son zama ‘yan Nigeria.

Dakta Shuaib Begore, babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, ya sanar da hakan a Abuja.

Matasa daga Nigeria kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen duniya musamman turai.

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta sanar da cewa jimillar mutane 38,051 ‘yan kasashen ketare ne suka mika takardar nuna sha’awar zama ‘yan Nigeria daga watan Satumba na shekarar 2018 zuwa watan na shekarar 2020.

Babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Belgore, ne ya fadi hakan yayin wani taro a Abuja, kamar yadda tribune ta rawaito.

Ta bayyana cewa ma’aikatarsu ta samu takardun masana’antu 45,751 da ke son matsaguni da Kuma mutane 38,051 da ke son gwamnati ta sahale musu su zama ‘yan Nigeria.

Dumbin matasa daga Nigeria da sauran kasashen nahiyar Afrika kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen ketare, musamman Turai da sauran wasu kasashe da suka samu cigaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here