An Kashe Fursunoni 129 da su kai Yunƙurin Tserewa a DR Congo
Ministan cikin gida na Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, Jacquemain Shabani Lukoo, ya bayar da rahoton cewa, fursunoni 129 ne aka kashe a wani yunƙurin tserewa daga gidan yarin Makala da ke Kinshasa, wanda shi ne gidan yari mafi girma kuma mafi suna a ƙasar.
Daga cikin waɗanda suka mutu, an harbe 24, yayin da wasu suka mutu sakamakon shaƙe musu wuya da aka yi da kuma turmutsutsu.
Read Also:
Lamarin ya kuma yi sanadin raunata mutum 59 a gefe guda kuma an yi wa mata da yawa fyaɗe.
Gobara ta kuma lalata wasu muhimman cibiyoyin gidan yarin da suka haɗa da gine-ginen gudanarwa da ma’ajiyar abinci.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin kisan gilla da aka yi a lokacin tserewa daga gidan yarin.
Ƙungiyoyin sun yi amannar cewa cunkoson fursunoni 14,000 a gidan yarin wanda aka gina da zai iya ɗaukar fursunoni 1,500 kaɗai ne ya haddasa tarzomar.