An Kashe Jami’in Hukumar DSS a Jahar Imo
An hallaka wani jami’in hukumar DSS a Owerri babban birnin jahar Imo.
Mr Deacon Daniel Opara, dan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa.
Amma ‘yan uwansa na zargin lauje cikin nadi duba da cewa an masa karin girma a baya-bayan nan.
Imo – An yi wa jami’in hukumar yan sandan farin kaya DSS, kisar gilla a garin Owerri, babban birnin jahar Imo, Daily Trust ta rawaito.
Hakan na faruwa ne kasa da awa 48 bayan kona ofishin hukumar da aka yi a Nnewi, jahar Anambra.
Wakilin Daily Trust ya rawaito cewa an bindige jami’in mai suna Prince Nwachinaemere Ezemuonye Ozuzu, daga Umuoyo, Irete, karamar hukumar Owerri West a hanyar Owerri/Onitsha.
An ce an tura jami’in ya yi wani aiki ne a Anambra awanni kadan bayan kona ofishin DSS na Nnewi.
Read Also:
An kashe shi ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta komawa wurin aikinsa.
A halin yanzu babu cikakken bayanin kan yadda ya mutu duba da cewa wani rahoton ya ce ya mutu ne sakamakon kuskuren harbi.
An ce wani abokin aikinsa ne ya harba bindiga bisa kuskure kuma harsashin ya same shi. Daya daga cikin yan uwansa, Deacon Daniel Opara, wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.
Ya ce:
“Ba mu samu cikaken bayani kan ainihin abin da ya faru ba domin an yi ikirarin cewa wani dan sanda da suke aikin hadin gwiwa tare ne ya bindige shi bisa kuskure a wurin aiki a jahar Anambra.
“Iyalansa na zargin akwai lauke cikin nadi duba da cewa a baya-bayan nan aka yi masa karin girma.
“Ya fara aiki da DSS kimanin shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata kuma yana da aure da ‘ya’ya hudu.”
Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar, CSP Mike Abattam ba domin wayansa ya yi ta ringing amma bai daga ba.