Sheikh Tijjani Kalarawi ya yi Murabus Daga Kwamitin Masallacin Fagge

 

Fitaccen Malamin musulunci a jahar Kano ya ajiye mukaminsa a masallacin Fagge.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya yi hakan saboda batun gina shaguna a masallacin.

‘Yan majalisar dokokin Kano sun tsoma bakinsu a lamarin, za a binciki badakalar.

Kano – Da jin babban malamin nan, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya bada sanarwar yin murabus daga kwamitin masallacin Fagge, majalisa ta shiga maganar.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2021, cewa ‘yan majalisar dokokin jahar Kano sun hana a gina shaguna jikin masallacin Juma’an.

Wani mataki ‘Yan majalisa suka dauka?

Shugaban majalisar dokoki na jahar Kano, Rt. Hon. Hamisu Ibrahim Chidari ya yi magana a dazu, ya bada umarnin a dakatar da gine-gine a harabar masallacin.

Honarabul Hamisu Ibrahim Chidari ya kuma kafa wani kwamitin mutum tara da zai duba lamarin.

‘Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne a sakamakon korafin da ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Dala, Hon. Lawan Hussaini ya kawo a zaman yau.

Hon. Lawan Hussaini yake cewa abin da ya faru da masallacin na Fagge, babban abin takaici ne.

Hakan ya jawo aka yi ta muhawara a zauren majalisar jahar.

Muhammad Uba Gurjiya mai wakiltar Bunkure ne zai jagoranci wannan kwamiti tare da Sunusi Usman Bataiya, Magaji Dahiru Zarewa, da dhi Lawan Hussaini.

Sauran ‘yan kwamitin sune:

Nuhu Abdullahi Achika, Abubakar Dalladi Isa Kademi, Muhammad Tukur da Sale Marke, sai wani jami’i a matsayin sakatarensu.

Badakalar filaye a Kano

Jaridar tace an dade ana samun badakalar filaye irin wannan a jahar Kano a ‘yan shekarun bayan nan.

Kamar yadda Kano Focus ta fitar da rahoto, Sheikh Kalarawi ya sauka daga mukamin da ya dade a kai bayan jin an bada filin masallaci domin ayi wasu shaguna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here