Bishiya Mai Shekaru 100 ta Fado Kan Jariri da Mahaifiyarsa  ta Hallaka su

 

Wata bishiya mai yawan shekaru ta fadi, inda ta fado kan wasu mutane da ke karkashin ta suka mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa, bishiyar ta kai shekaru 100 a yankin, lamarin kuma ya girgiza mutane.

Wani mutum ya jikkata, wanda tuni aka dauke shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa.

Oyo – Mutane hudu ne ake fargabar sun mutu yayin da wani kuma ya samu munanan raunuka a lokacin da wata tsohuwar bishiyar ” Odan” ta fadi sakamakon guguwa mai karfi a yankin Saabo da ke cikin garin Oyo a ranar Litinin, Premium Times ta rawaito.

Tsohuwar bishiyar ta ba da mafaka ga mahauta, kananan motoci da matuka baburan kasuwanci tare da rassanta da suka yadu a mashahurin kasuwar kayan abinci a cikin garin Oyo.

Akeebu Alarape, Shugaban Kasuwar Saabo ta garin Oyo, ya shaida wa NAN cewa bishiyar ta kai kimanin shekaru 100.

Mista Alarape ya ce wasu masu aikin yankan bishiya hudu da aka gayyata don sare bishiyar ba su yi nasara ba har sai da na biyar ya zo tukuna ya sami damar yanke wasu sassansa don fara aikin ceto.

Wata ‘yar kasuwa mazauna yankin, Kareemot Ejide, ‘yar shekara 65, ta ce ta san bishiyar tun tana yarinya.

A cewar Akeem Ojo, shugaban hukumar tsaron yankin Yarbawa ta “Amotekun” a yankin Ci gaban Karamar Hukumar Atiba, bishiyar ta fadi ne da misalin karfe 6 na yamma.

A cewar Ojo:

“Wata daliba mace a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Special), Oyo, wata mata da jariri daure a bayanta da wani yaro da take rike da shi an ciro su daga gindin bishiyar.

“Mutum daya ya samu munanan raunuka kuma an kai shi wani asibiti mai zaman kansa a yankin, yayin da babura da wuraren hutawa na karkashin bishiyar suka lalace.”

Ya kara da cewa kasancewar Amotekun a wurin da abin ya faru shine hana tarzoma da sace kayan ‘yan kasuwa a kasuwar.

Dalilin faduwar bishiryar

Shugaban yankin ci gaban Karamar Hukumar Sooro, Oke-Isiwin, Oyo, Seun Oguntona, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN cewa wadanda abin ya shafa mutane ne da suka fake a karkashin bishiyar yayin ruwan sama mai karfi.

Ya kara da cewa wadanda ke kasuwanci a karkashin bishiyar za a mayar da su wurin daban.

Ya bukaci mutanen yankin da su kasance a ko da yaushe cikin gida kuma kada su fake a karkashin bishiyoyi lokacin da ake ruwan sama.

Ya karyata jita-jitar cewa itaciyar tsafi ce, ya kara da cewa wanda ya dasa ta ya mutu shekaru 30 da suka gabata.

Mista Oguntona ya ce duk da cewa mutumin ya kasance mai riko da addinin gargajiya na “Sango”, ya dasa bishiyar ne don bai wa mutane inuwa.

Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jahar Oyo, Adewale Osifeso, bai ci nasara ba saboda bai dauki wayar ba sadda aka kirashi, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here