An Kama Direban Da ke Mika Fasinjoji Hannun Masu Garkuwa a Kano

 

‘Yan sandan Najeriya sun kama wani direban motar haya da ake zargi da yaudarar fasinjoji zuwa wurin masu garkuwa da mutane a Jahar Kano da ke arewacin Najeriya.

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana matashin mai shekara 25 a matsayin ɗaya daga cikin wani gungun mutum 11 da ke aikata garkuwa da mutane.

Yayin da ake gabatar da su ga manema labarai a Abuja ranar Talata, ‘yan sanda sun ce gungun ya ƙunshi maza tara da mata biyu, waɗanda ke gudanar da ayyukansu a tashoshin mota biyu da ke Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Najeriya Frank Mba ya ce dakarunsu sun yi nasarar ƙwace bindigar Ak-47 biyu da harba-ruga biyu da kuma wasu makaman daban daga hannunsu.

“Nakan hau motar a matsayin fasinja, wani lokacin kuma na tuƙa tawa motar,” a cewar Bashiru Sule, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin.

“Ina yin lodi a tasha sannan kuma na faɗa wa masu garkuwa da mutanen labarin mutanen da na ɗebo a motar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here