An Kashe Sama da Jami’an Tsaro 326 – Rahoto
Abuja – Akalla jami’an tsaro 326 ne aka ce sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin su a tsakanin Janairun 2023 zuwa Janairun 2024.
Jami’an da aka kashe sun fito daga hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da ƴan sanda, NSCDC, hukumar shige da fice, da sojojin Najeriya.
‘An kashe sama da jami’an tsaro 326’ – Rahoto
Sai dai rahoton da jaridar Punch ta fitar ya ce akwai yiwuwar adadin na iya wuce 326, tunda an tattara alkaluman ne daga rahotannin kafafen watsa labarai.
Read Also:
Rahoton ya nuna cewa rundunar ƴan sanda ce ta rasa jami’ai mafi yawa, inda aka kashe ‘yan sanda 258 a tsakanin 2023 zuwa 2024.
A bangaren rundunar sojoji, da ta hada da ta rundunar sojin kasa, sama da ruwa, an rasa sojoji 59, yayin da NSCDC ta rasa jami’ai biyar.
Yadda aka kashe sojoji da dama a Najeriya
Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ita ce ta samu ƙarancin hasarar jami’ai, inda aka kashe jami’anta hudu, a cewar rahoton.
Da rahoton ya fadada bayani, an ji cewa a watan Janairun 2025, an kashe sojoji 22 a wata mummunar arangama da ƴan ta’adda.
A watan Maris din 2024 kuwa, an kashe sojoji 17 a harin ƴan bindiga a garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.