An Kashe Mutane 81 a Mafa

 

Hukumomi a jihar Yobe da ke arewa masu gabashin Najeriya sun tabbatar da cewa an kashe mutum aƙalla 81 a harin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a garin Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa.

A ranar Talata, mai magana da yawun ƴansanda a jihar Yobe, Abdulkarim Dungus ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “mayaƙan da ake zargin ƴan Boko Haram ne kimanin 150 a kan babura ne suka dirar wa garin na Mafa, ɗauke da manyan makamai a ranar Lahadi.”

Ya ƙara da cewa maharan sun “kashe mutane da dama da ƙona shaguna da gidaje, sai dai har yanzu ba mu kammala tattara ɓarnar da suka yi ba.”

Sai dai wani jami’i, Bulama Jalaludden ya bayyana cewa “mun tabbatar da cewa an kashe aƙalla mutum 81 daga lissafin da muka yi.

A yau Talata ne aka gudanar da jana’izar wasu daga cikin mutanen da suka rasu a harin na ranar Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here