An Kashe Mutane 124 a Cikin Mako ɗaya a Sudan
Wata babbar jami’ar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rahotannin kashe-kashe, ciki har da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a jihar Gezira da ake zargin dakarun RSF da yi akwai ɗaga hankali.
Read Also:
Jawabin na Clementine Nkweta-Salami ya zo ne bayan wata ƙungiyar fafutika a ƙasar Sudan ta ce aƙalla mutum 124 ne dakarun RSF suka kashe a cikin mako ɗaya.
Sai dai ita RSF ta ce ba ka tai hare-hare kan fararen hula, inda ta nanata cewa tana kai hare-haren ne kan sojoji da masu ƴanbindiga.
Yaƙin na Sudan wanda ya kwashe sama da wata 18 zuwa yanzu, ya ci dubban mutane, kuma ya raba sama da mutum miliyan 11 da muhallansu.
Yanzu jihar Gezira ce ta zama filin daga daga makon jiya bayan wani kwamandan RSF, Abu Aqla Kayka ya koma ɓangaren sojoji.