Adadin Mutanen da Aka Kashe a Zanga-Zangar Bangladesh
Masu zanga zanga a Bangladesh na kira ga Firaimistan kasar Sheikh Hasina ta sauka daga mukaminta, yayin da dubban masu zanga zangar suka hallara don maci zuwa Dhaka.
Halin da ake ciki a babban bbirnin kasar ba dadi domin ana cikin zaman dar-dar.
Gwamnatin kasar ta sanar da hutun kwanaki uku inda aka rufe dukkan harkokin kasuwanci da kuma kotuna.
Read Also:
An toshe hanyar shiga Dhaka, inda aka tsaurara matakan tsaro a sassan birnin, sannan an sake dauke intanet a wasu sassan na kasar.
A jiya Lahadi an kashe mutum fiye da casa’in a gwabzawar da aka yi da jami’an tsaro ciki har da jami’an ‘yan sanda da dama.
A watan da ya gabata ne aka fara bore saboda sabon tsarin da gwamnati ta fito dashi na rabon guraben aiki abin da bai wa ‘yan kasar musamman dalibai dadi ba.