An Kashe Sojojin Isra’il 8 a Artabu da Hezbollah

 

Isra’ila ta ce sojojinta takwas aka kashe a Lebanon yayin da dakarunta ke ci gaba da faɗa da mayaƙan Hezbollah ta ƙasa.

Tun da farko rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun yi artabu da Hezbollah.

Isra’ila ta tura dakaru a kan iyaka da Lebanon domin yaƙi da Hezbollah

Isra’ila ta yi gargaɗi ga ƙauyuka 20 a kudancin Lebanon su fice daga gidajensu, tare da ƙara nanata gargaɗin bayan ta fara gwabza faɗa ta ƙasa.

Hukumomin lafiya na Lebanon sun ce mutum 55 aka kashe a sassan ƙasar a hare-haren Isra’ila ta sama a ranar Talata.

Tun da farko rundunar sojin ta tabbatar da kashe kwamandanta.

Hezbollah ta bayar da rahoton cewa ta yi arangama da sojojin Isra’ila a aƙalla garuruwa biyu da ke kan iyaka da Isra’ila, inda ta kuma sha alwashin korar dakarun na Isra’ila daga yankin.

A wajen taron masu ruwa da tsaki na Iran, shugaban addinin Iran ya ce dole ne ƙasashen yammaci su fice yankin Gabas ta Tsakiya domin samun zaman lafiya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here