Ɗan Baiwa Haihuwar Sa’a : Malam kashifu Inuwa Abdullahi Shugaba Abin Koyi
Jagora Nagari! Ƙarfin dogaro ga Allah Ya na daga sirrin samun nasarar Malam Kashif Inuwa a rayuwa, mutum ne wanda Allah Ya tsaye masa a rayuwarsa duba da cewa abubuwa da dama na cigaban rayuwa ba wai nema ya ke yi ba amma Allah Ya ke ba shi, ƙaramin misali shi ne muƙamin shugabancin hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA).
A wani lokaci da ya ke zantawa da mane labarai shi da kansa ya labarta cewa wannan muƙami ko matsayi na shugabancin hukumar, ya na ɗaya daga cikin abubuwa na kwatsam da su ka faru da shi a rayuwarsa wanda bai zata ba, bai kuma nufa ba amma Allah Ya ba shi.
Haka zalika, Malam Kashif Inuwa Damo ne wajen haƙuri, haƙuri kuwa babbar ni’ima ne, kana baiwa ce, duk bawan da Allah Ya ba wa haƙuri ya gode masa domin babu wanda Ya isa ya ga bayansa balle ya durƙusar da shi, saboda Allah ne da kansa Ya ce Ya na tare da su (masu haƙuri), haƙuri halin Manzon Allah ne (S.A.W).
Read Also:
Bugu da ƙari, Malam Kashif Inuwa Abdullahi matashi ne mai ɗumbin ilimi, mai hangen nesa, mai kaifin ƙwaƙwalwa gami da juriya da ƙwazo matuƙa. Duk waɗannan abubuwa da ya siffanta da su, sinadarai ne da ke taimakawa ɗan adam wajen samun nasarar duk wani abu da ya sa a gaba. Ƙaramin misali shi ne yadda ya yi aiki tuƙuru a waɗannan shekaru uku bisa kan wannan matsayi ya sanya mai girma minista, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), alfahari, ya sanya mai girma shugaban ƙasa, Malam Muhammadu Buhari (GCFR) alfahari, ya sanya jama’ar Jihar Jigawa da ƴan Nageriya alfahari, kowa yau sambarka ya ke yi.
Dama ya faɗa cewar Insha Allahu zai yi duk mai iyuwa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa a wata zantawa da ya yi da mane labarai ƴan kwanaki kaɗan da samun matsayin, domin ya ga ya ƙarfafawa kowa gwiwa tayadda kuma hakan zai cigaba da sanya yaƙini da amanna a kan matasan ƙasar nan idan an ba su dama.
Yau kowa alfahari ya ke yi da Malam Kashif Inuwa a ciki da wajen Nageriya balle kuma aka shigo gida Jihar Jigawa, wannan kuma shi ke ƙara ƙarfafawa jama’a gwiwa a kansa su ke cigaba da yi masa fatan alkhairi domin ya yi an gani bai bada kunya ba, Ya zama abin alfaharin.
Wannan kuma shi ke ƙara nuni da yadda zai yi duk mai iyuwa wajen sauke duk wani nauyi da zai hau kansa batare da ya bayar da kunya ba.
Khairan Insha Allah.
Garba Tela Haɗejia
Litinin, 9 ga watan Maris, 2022.