Jakadan Jigawa: Malam Kashifu Inuwa Abdullahi: Hantsi Mai Leka Gidan Kowa
Al’ummar Jihar Jigawa daga ɓangarori daban-daban, sun gamsu, sun yarda, sun yi imani cewa mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), Damo sarkin haƙuri, Agogo sarkin aiki, shi ne ya buɗe sabon babi na nuna so da ƙauna gami da rungumar kowa da kowane yankin Jihar bisa damar da ya samu a tarayya wanda hakan ke nuni da shi ɗan jakada ne nagari ga Jihar Jigawa ba wai iya yankinsa ba.
A yau duk inda ka bincika ka duba a faɗin Jihar Jigawa sai ka gano ɗumbin ayyukan alkhairan da ya shimfiɗa in ma a ƙarƙashin hukumar ta (NITDA) da ya ke jagoranta ko kuma ta ƙarƙashin gidauniyarsa ta taimakon al’umma (Malam Inuwa Foundation), ko ma duka biyun.
Wannan ɗabi’a da halayyar ƙaunar kowa da kowane yanki da ya ke nunawa duk al’ummar tsawon shekaru uku a wannan muƙami, shi ke ƙara zaburar da al’ummar wannan Jiha wajen cigaba da yin amanna da shi gami da yi masa addu’ar cigaba da samun nasara da ɗaukaka.
Duk inda ka duba cikin kowane rukuni na al’ummar wannan Jiha yabonsa su ke, masu martaba iyayen ƙasa, (sarakuna) sun yi imani shi ɗin matashi ne mai dattako da cikar duk wata kamala, kana kuma mutum ne wanda ya yi imani da haɗin kan al’ummar Jihar Jigawa da damawa da kowa cikin duk wata damarsa.
A wata ziyarar girmamawa da ya taɓawa kaiwa mai martaba sarkin Dutse, Alhaji Dakta Nuhu Muhammad Sunusi, (CON), mai martaba sarki ya yi bayanin cewa, Kashifu shi ne ɗaya ɗaya tilo da ya samu dama a gwamnatin tarayya kuma ya ke amfani da damar tasa wajen amfanar da al’ummar Jihar Jigawa gabaɗaya.
Haka zalika, mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gumel na yanzu, Comrade Ahmad Rufa’i Gumel, a ya yin wata ziyarar girmamawa da mu ka kai masa a ƙarƙashin ƙungiyar BNMC, ya taɓa faɗa cewa Malam Kashif Inuwa shi ɗin nadaban ne a Jigawa domin duk yawancin mutane idan su ka samu dama to su na amfani da wannan dama ne ta amfane su, su kaɗai da ƴan garinsu kawai, amma shi ya rungumi kowa.
Read Also:
Daɗi da ƙari, shi ma Buhari Ya’u Gumel, cewa ya yi, “shi fa wannan bawan Allah, (Malam Kashif Inuwa Abdullahi) da ku ke gani, shi ɗaya ne tal! Babu na biyunsa ɗan Jahar Jigawa wanda mu ke da shi ya ke wakiltar jihar a matakin gwamnatin tarayya wanda babu wata ƙaramar hukuma da ta ke Jigawa da za ka zo ba ka ga aikin alkairinsa ba. Tun daga kan minista, har zuwa ƙasa da minista tunda aka kafa Jigawa da sunan Jiha har zuwa yau din nan ba a taɓa samun wata kujera wadda kusan dukkan ƴan Jihar su ka amfana irin ta wannan bawan Allah, shugaban hukumar (NITDA), Malam Kashif Inuwa ba, idan kuma akwai to a gaya mana don mu sani. Wannan shi ne ya sa mu ke yi wa wannan bawan Allah Addu’a da kuma fatan alkairi, Allah Ya sa likkafa tafi ta yanzu. Amin Ya Hayyu Ya Qayyum”. -B. Gumel.
Haka zalika, matashin ɗan gwagwarmaya daga yankin masarautar Kazaure, (Adamu Kazaure) a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook jiya mai taken: “Jihar Jigawa A 2023”, a cikin rubutun ya bayyama cewa: “Tabbas nagartar Malam Kashifu Inuwa, da gogewarsa, da hangen nesansa, da kuma jajircewarsa sun isa su sa ya zo ya ja ragamar shugabancin wannan Jiha tamu. Muna da kyakkyawan sa rai akansa na cewa duk wani abu da muka rasa a baya, to zamu same shi a gaba, idan Allah (S.W.T) ya ba shi dama zai yi shugabanci daidai da zamani”.
Adamu Kazaure ya kuma cigaba da cewa: “dattakon sa zai taimaka wajen haɗa kan al’ummar wannan Jiha tamu, mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya. Za kuma mu samu gagarumin cigaba a ɓangarori da dama. Ya Allah! Ka tabbatar mana da Malam Kashifu Inuwa a matsayin sabon Gwamnan jihar Jigawa. Amin”. Cewar Adamu Kazaure.
Duk inda za ka tuntuɓa ko ka saurara daga ra’ayoyin al’umma daban-daban daga kowane sashe na Jihar Jigawa alkhairan Malam Kashif Inuwa su ke faɗa gami da yi masa fatan alheri.
Wannan kuma wata ƴar manuniya ce da ke nuni da yadda Malam Kashif Inuwa ya zama jakadan Jihar Jigawa a tarayya ba wai yankin da ya fito kawai ba, kana kuma shi ɗin na zaman tamkar hantsi mai leƙa gidan kowa wanda zai cigaba da yi da kowa a duk wata dama ta alkhairi da zai samu a rayuwarsa.
Khairan Insha Allah.
Garba Tela Haɗejia
8 ga watan Maris, 2022.