Katin Daurin Auran Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Bayero

 

Tun a makon da ya gabata ne aka fara shirin auren dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Bayero Katin daurin auren ya bayyana inda za a daura a ranar Juma’a, 20 ga watan Augusta, da karfe 1:30 na rana Za a dauran auren soyayyan ne a fadar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero dake garin Bichi a jahar Kano.

Bichi, Kano – Ana shirye-shiryen shagalin bikin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.

An fara bikin ne tun a makon da ya gabata inda aka fara da wasan Polo tare da wankan amarya, lamarin da ya janyo cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama’a.

Kwatsam a yau Juma’a, 13 ga watan Augusta, sai ga katin daurin ya bayyana inda @BBCHausa ta wallafa a shafinta na Instagram.

Bayanan da katin ya kunsa

Kamar yadda katin ya nuna, za a yi daurin auren a ranar Juma’a, 20 ga watan Augusta wanda yayi daidai da 12 ga watan Muharram, shekara 1443 bayan hijirar Annabi Muhammadu S.A.W.

A saman katin an fara saka tambarin kasa kafin daga bisani a zayyano sauran bayanai kamar haka:

Iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR da na Mai Martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi, suna farin cikin gayyarku zuwa wurin daurin auren dansu da ‘yar su, Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero.

Wanda aka shirya za a yi kamar haka: Rana: 20 ga watan Augustan 2021, daidai da 12 ga watan Muharram, shekara 1443 bayan hijira.

Lokaci: Karfe 1:30 na rana Wuri:

Fadar Sarkin Bichi, Bichi, jahar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here