Rigakafin Corona: Dokar Dakatar da Ma’aikatan da Basu da Katin Shaida ta Fara Aiki a Jahar Edo
Jami’an lafiya tare da haɗin kan jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki kan rigakafin corona.
Gwamnan ya sanar da shirin gwamnatinsa na dakatar da duk wani ma’aikaci da bai yi allurar rigakafin COVID19 ba daga zuwa aiki.
Wasu hotuna da suka fito daga jahar sun bayyana yadda ma’aikata ke nuna katin shaida kafin shiga kowace ma’aikata a Benin.
Edo – Gwamnatin jahar Edo, karkashin jagorancin gwamna Obaseki ta fara aiwatar da dokar “Ba rigafin korona, babu aiki” a ma’aikatun jahar, kamar yadda dailytrust ta rawaito.
Gwamna Obaseki na jahar Edo, shine gwamna na farko a Najeriya da ya hana mutanen da ba’a musu rigakafin cutar COVID19 ba shiga wuraren gwamnati.
Read Also:
Duk da cewa da farko an yi watsi da kudirin gwamnan, amma Obaseki bai yi kasa a guiwa ba wajen aiwatar da kudirinsa.
Su wa ke hana mutane shiga ma’aikatu?
A ranar Laraba da safe, jami’an lafiya da kuma jami’an tsaro sun kafa madakata a kofar shiga ma’aikatun Benin, Babban birnin jahar, inda suke tabbatar da an bi umarnin gwamna.
Ba damar shiga sakateriyar gwamnati a Edo sai da kati
Punch ta rawaito cewa an hana duk wani ma’aikaci da ya gaza gabatar da katin shaidar allurar rigakafin COVID19 shiga sakateriyar gwamnatin Edo.
Gwamnatin ta fara aiwatar da shirinta na hana taruwar mutane da yawa ba tare da shaidar karɓar rigakafi ba.
Lamarin wanda ya fara da karfe 7:00 na safiyar Laraba, yasa an hang shugaban kwamitin yaƙi da COVID19 na jahar, Yusuf Haruna, ya tare babbar kofar shiga sakateriyar wacce ta yi hannun riga da ofishin EFCC.