Gwamnatin Jahar Katsina Zata Hana Kiwon Fili

 

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, yace gwamnatinsa zata diba yiwuwar hana kiwon fili a faɗin jahar.

Masari ya bayyana cewa kafin kafa dokar gwamnati zata samar da filin kiwo ga makiyaya.

A cewarsa, Gwamnatin tarayya ta turawa Katsina biliyna N6.2bn, kuma a matakin jaha za’a zuba wasu kuɗaɗen.

Katsina – Gwamna Aminu Bello Masari na jahar Katsina, yace gwamnatinsa zata duba yuwuwar hana makiyaya kiwon fili a faɗin jahar.

Masari ya yi wannan jawabi ne a cikin shirin ‘Politics Today’ na kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Litinin.

Gwamnan ya yi watsi da yadda makiyayan suke yawo daga wannan yankin zuwa wani a faɗin ƙasa.

Sai dai ya bayyana cewa kafin gwamnatinsa ta hana makiyaya kiwon dabbobinsu a fili, sai ta tabbatar ta samar musu wurin da zai zame musu gida, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Shin kiwon fili ya saba wa musulunci?

A jawabinsa, Masari yace:

“Muna kokarin hana makiyaya yawo da shanu a fili, amma kafin mu kafa dokar zamu tabbatar mun samar musu da wurin kiwo.”

“Kamata ya yi makiyaya su zauna a wuri ɗaya, yawo da dabbobi ko ina ba abu bane mai kyau, ina tunanin ya sabawa addinin musulunci.”

“Me zai sa ka mallaki dabbobin da ba zaka iya ciyar da su ba? kuma ka dinga zuwa gonakin mutane kana musu ɓanna kuma kace shin hakan dai-dai ne? Bana tunanin haka abu ne mai kyau.”

Wane mataki Masari zai ɗauka?

Bugu da kari Masari yace a kokarin da suke na fara shirin zamantar da kiwon dabbobi, gwamnatin tarayya ta turo biliyan N6.2bn. Gwamnan yace:

“Mun dade da fara aiwatar da shirin, FG ta bamu biliyan N6.2bn kuma munanan a matakin jaha zamu zuba biliyan N6.2bn. Manufar mu itace mu samar wa fulani wuri ɗaya da zasu zauna.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here