‘Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Direktan NBC, Ahmed Abdulkadir da Yarsa a Jahar Katsina

 

Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon direktan NBC, Ahmed Abdulkadir da yarsa a Katsina.

Hakan na zuwa ne kasa da awa 24 bayan wasu yan bindigan sun sace iyalan dan majalisar dokokin jahar Katsina.

Baya ga tsohon direktan, yan bindigan sun sace wasu mutane uku amma sun sako su bayan yan banga sun yi musayar wuta da su.

Katsina – Kimanin kwana guda bayan sace iyalan dan majalisar dokokin jahar Katsina, ‘yan bindiga sun sake sace wasu mutanen a jahar.

A cewar rahoton Daily Trust, a daren jiya, yan bindigan sun kai hari rukunin gidaje na Bakori sun sace wani Alhaji Ahmed Abdulkadir, tsohon direktan NGC da yarsa mai shekaru 15 mai suna Laila.

Yan bindigan da suka taho da AK-47 sun kuma sace wasu mutane guda uku. Sun kai hari gidajen wadanda abin ya faru da su ne misalin karfe 9 na dare a cewar majiyoyi kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Sauran da aka sace sun hada da Alhaji Bello Aminu Bakori, Shamsuddeen Aminu da wani Habibu Rabe ma’aikacin hukumar Ilimi, Bakori.

‘Yan banga sun ceto mutane uku daga hannun ‘yan bindigan

Jim kadan bayan sace su, ‘yan banga da ke unguwar sun taru sun bi sahun bata garin da nufin ceto wadanda aka sace.

‘Yan bangan sun cimma yan bindigan a karamar hukumar Danja kuma bayan musayar wuta sun sako uku cikin wadanda suka sace.

Amma Abdulkadir da yarsa har yanzu suna nan hannun masu garkuwar.

‘Yan bindigan sun saka mutane cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren da suke kai wa a yankunan kasar.

Daga Abuja, zuwa Zamfara, Niger, Kaduna da wasu wuraren da dama, yan bindigan su kan kutsa gidajen mutane su sace su domin karbar makuden miliyoyi na fansa.

ALLAH ya Kawo Mana Karshen su.Ameen

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here