Jahar Katsina ta Hana Makiyaya Kiwo a Fili

 

Kamar sauran jahohi, jahar Katsina ta shiga jerin jahohin da suka hana kiwon fili.

Gwamnatin Buhari ta baiwa jahar Katsina biliyoyi don kiwon zamani.

Jahar Katsina na fama da matsalar rashin tsaro.

Masarautar Katsina ta ce daga yanzu an haramta kiwon Shanu a fili a cikin garin jahar da kewaye.

Wannan na kunshe cikin rahoton Katsina Post da gidan talabijin KatsinaTV, ranar Laraba.

A cewar rahoton, Wakilin Kudin Katsina, Alhaji Abdu Iliyasu, wannan haramci zai fara ne daga ranar Talata, 3 ga Agusta, 2021.

Ya kara da cewa an shirya komai domin tabbatar da an dabbaka wannan doka.

Amma, mai magana da yawun masarautar Katsina, Malam Iro Bindawa, yace ba zai iya magana kan haka ba saboda ba ya gari, amma zai yi idan ya dawo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here