Gwamnatin Jihar Katsina ta Magantu Kan Neman Sulhu da Ƴan Bindiga

 

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa ba za ta tattauna da ‘yan bindiga don neman sulhu ba.

Kwamishinan tsaro da harkokon cikin gida, Mu’azu Ɗanmusa ya jaddada kudirin gwamnatin Dikko na kawo karshen ‘yan bindiga a jihar.

A cewarsa, kaddamar da sabuwar rundunar ‘yan sa’kai alama ce ta zahiri da ke nuna yadda Radɗa ya maida hankali kan tsaro.

Jihar Katsina – Gwamnatin jihar Katsina ta ce ba za ta tattauna da duk wani ɗan ta’adda ko kungiyar ‘yan bindiga ba, amma za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare al’umma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Muazu-Danmusa, ne ya bayyana haka a wata hira da hukumar dillancin labarai NAN ranar Laraba.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin Malam Dikko Raɗda na ganin an kawo karshen ‘yan fashin daji da sauran matsalolin tsaro, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Muazu-Danmusa ya kuma ce gwamnatin na daukar matakan da suka dace domin bai wa ‘yan gudun hijirar jihar damar komawa garuruwansu.

Ya ce kaddamar da rundunar Community Security Watch Corps (KCSWC) da Gwamna Raɗɗa ya yi ranar 10 ga watan Oktoba, alama ce da ke nuna yadda ya ɗauki sha’anin tsaro.

An fara shirin maida ‘yan gudun hijira gidajensu A rahoton Premium Times, Kwamishinan ya ce:

“Ina tunanin jihar Katsina ce tafi kowacce jiha yawan ‘yan gudun hijira a yankin Arewa maso Yamma sakamakon rashin tsaro. Duk da haka, muna ƙoƙari canza labarin ta hanyar tsara dabarun za su magance matsalar.”

Muazu-Danmusa ya ƙara da cewa gwamnati ta tsara daidaita albashin dakarun KCSWC bisa tsarin mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

“Muna kan gina musu ofisoshi, mun ba su motocin sintiri, babura, makamai da sauran kayan aiki domin inganta ayyukansu.”

“Muna tafiya daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan wajen samar musu da dukkan wadannan abubuwa,” In ji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa dakarun rundunar sun shirya tsaf wajen yin wannan aiki na sadaukar da rayuwarsu domin kare dangi da al’ummarsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com