Katsina: Rundunar ‘Yan Sanda ta Cafke Wasu Manyan ‘Yan Fashi
Yan sandan jihar Katsina sun gurfanar da wasu kasurguman yan bindiga.
Har ila yau rundunar yan sandan ta baje kolin wani dillalin dalar Amurka na bogi.
An yi nasarar cafke miyagun ne bayan samun wasu muhimman bayanai na sirri Rundunar yan sandan jihar Katsina ta gurfanar da wasu bindiga biyu da ta kama, masu fashi da makami da wani dillalin dalar Amurka na bogi a Katsina.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya fada ma manema labarai cewa an kama manyan yan fashin biyu masu suna: Idi Sabi’u Dila, 30, da dayan da ba’a san sunansa ba.
Read Also:
An kama su ne a kauyen Mununu, karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, bayan an samu bayanai abun dogaro, jaridar The Nation ta ruwaito.
Ya ce: “Dan bindigan ya hadu da bacin rana ne lokacin da aka kama shi a Sheme a hanyarsa ta zuwa Faskari.
A yayin bincike, mai laifin ya fallasa cewa shi dan kungiyar yan bindiga ne na wani Melaya Alhaji Gandu na dajin Munhaye, karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.
“Hakazalika, mai laifin ya tona cewa da shi aka kai hare-hare a kauyen Kadisau, karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina a ranar 9 ga watan Yulin 2020 wanda ya yi sanadiyar kashe jama’a da dama da kuma hare-hare makamantan haka a jihohin Katsina da Zamfara.”
Kakakin rundunar ya kuma gurfanar da wasu manyan yan bindiga da ke addabar kananan hukumomin Safana da Jibia