2027: Yadda Kawancen ‘Yan Adawa za ta kai ga ci – Atiku
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fadi yadda kawancen ‘yan adawa za ta kai ga ci.
Ya bayyana cewa za su rungumi kowane dandali da zai tabbatar da manufarsu ta kyakkyawan shugabanci domin kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
A wani bidiyon taron da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, Atiku ya tabbatar da cewa jirgin kawancen jam’iyyu ya bar tasha, kuma zai tsaya a wurare da dama domin daukar ‘yan Najeriya.
Atiku ne ya bayyana hakan ne yayin wani taro da wata tawaga ta National Opinion Leaders, kwana biyu bayan Kungiyar Gwamnonin PDP ta nesanta kanta da hadakar jam’iyyunsa.
Shawarar Atiku ga matasa kan zaben 2027
Daily Trust ta wallafa cewa a yayin da yake jawabi ga tawagar National Opinion Leaders da yawansu matasa ne, Atiku ya bukace su da su gujdewa ruɗin kyautar kudin da bai taka kara ya karya ba.
Ya ce:
Read Also:
“Kada ku bari a ruɗe ku da wasu kudade kaɗan da ake bayarwa, har ku yarda ku sayar da makomarku da makomar ‘ya’yanku.”
“Saboda haka ne wasu daga cikinmu shugabanni daga jam’iyyun da na ambata – APC, PDP, LP da sauransu – muka yanke shawarar cewa za mu samar da abinda nake kira da Hausa ‘Sabuwar tafiya’, wato a Turance, a new path – wata sabuwar hanya zuwa sabuwar Najeriya.”
“Mun fara ganawa, kuma da ikon Allah, ba da jimawa ba za mu bayyana wannan sabuwar tafiya, muna kuma fatan ku matasa ku kasance a cikinta.”
Atiku ya fadi manufar kawancen jam’iyyu
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce babban burin wannan kawance shi ne samar da shugabanci nagari.
Ya ce:
“Duk wata hanya da za ta ba mu damar samun kyakkyawan shugabanci don makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu, to wannan ce hanyar da za mu bi.”
“Ku fara tsara yadda za ku hada kai, ku kuma fara aiki tare domin samun karin ‘yan Najeriya da za su rungumi wannan sabuwar tafiya.”