Sudan: Bazan Tattauna da Kowa ba Har Sai an Kawo ƙarshen Rikicin ƙasar – Hemedti
Ɗaya daga cikin janar-janar ɗin sojin da ke faɗa da juna a Sudan, wanda ke jagorantar dakarun RSF ya shaida wa BBC cewa ba zai yi wata tattaunawa da kowa ba sai an kawo ƙarshen rikicin ƙasar.
Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya ce ana ta “jefawa” mayaƙansa bam tun da aka amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta.
Read Also:
Ya ce “Ba ma son a lalata Sudan,” sannan ya ci gaba da zargin Janar Abdel Fattah al-Burhan da tayar da zaune tsaye.
Janar Burhan ya tabbatar da zai amince a yi tattaunawar ido da ido tsakaninsu a Sudan ta Kudu.
An samu nasarar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ne a ranar Alhamis saboda shiga tsakani da ƙasashen duniya suka yi ta fuskar diflomasiyya da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya,
Da yake tattaunawa da BBC ta wayar tarho, Hemedti ya ce a shirye yake ya tattauna amma da sharaɗi – cewa sai an dakatar da yaƙi: “an dakatar da kashe-kashe. Sannan za mu shiga tattaunawar.”
Ya ce ba shi da wata matsala tsakaninsa da Janar Burhan, amma yana masa kallon maci amanar ƙasa.