A Shirye Nake Domin Kawo ƙarshen Rikicin Fulani – Sarki Sanusi II
Jihar Kano – Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin Fulani da ke faruwa a kasar nan.
Sarkin ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar har abada, yana mai cewa hakan ba za ta faru ba sai da taimakon gwamnatin tarayya.
Fulani sun ziyarci Sarki Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin kungiyar Fulani, ‘Tapital Pulaku Njode Jam Nigeria’ a fadarsa da ke Kano yau Talata, Punch ta tattaro labarin.
Read Also:
Muhammadu Sanusi II ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta samar da mafita ta din-din-din game da rikicin Fulani makiyaya da ya addabi sassan ƙasar nan.
Yadda za a kawo karshen rikicin Fulani
A rahoton Leadership, Sarki Sanusi II ya ce:
“Hakan za ta yiwu ne idan gwamnatin tarayya ta ba ni goyon baya saboda tana da ƙarfi da duk abin da ake bukata da har dabaru na za su yi aiki.
An yi watsi da Fulani kuma ba haka ya kamata ba, lokaci ya yi da gwamnati za ta haɗa kai da mu wajen samar da mafita musamman rikicin Fulani da manoma.”
“Ni a shirye nake na taimaka wa gwamnati ta cimma burinta na samar da zaman lafiya a tsakanin Fulani da sauran ’yan Najeriya, a daina cutar da su, ina da yaƙinin hakan zai yiwu.”
Sarki Sanusi II ya kara da musanta ikirarin cewa akwai bara gurbi a cikin Fulani, waɗanda suka shafa masu kashin kaji har ake masu kuɗin goro.