Abinda ya Kara kawo Matsalar Tsaro a Kasa – Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya bayyana daya daga cikin abubuwan da ke rura wutan matsalar tsaro.
Buhari ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimakawa mutan Karkara.
Buhari ya karbi bakuncin yan kasuwan taki a fadarsa dake Villa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin ayyukan yi cikin matasan Karkara ya zama babban kalubalen da ke rura wutan matsalar tsaro a Najeriya.
Buhari ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda karban bakuncin kungiyar masu sarrafa taki a Najeriya (FEPSAN), rahoton DailyTrust.
Read Also:
Shugaban kasan yace shekara da shekaru gwamnatocin da suka shude sun mayar da hankulansu kan raya birane maimakon raya Karkara.
“A tsawon shekaru hudu da suka gabata, mun yi aiki tukuru domin daidaita abubuwa ta hanyar inganta aikin noma da bayar da kudade domin samar da ayyukan yi a Karkara,” Buhari yace.
“Yayinda muke kokarin fadada yunkurin tabbatar da tsaro da dakile matsalar tsaro, ya nada muhimmanci in bayyana cewa ba za’a samu dawwamammen zaman lafiya da cigaba ba sai mun hada kai wajen samar da aikin yi ga mutan karkara.”
“Saboda haka ina kira ga gwamnoni, bankuna, da masu sanya hannun jari su rika shiga Karkara,” Buhari ya kara.