Gwamnatin Kebbi ta Sanya Hannu Kan Dokar Mafi ƙarancin Albashin N75,000
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya sanya hannu a kan sabuwar dokar tsarin albashi mafi ƙanƙanta – naira 75,000, ga ma’aikatan jihar.
A lokacin bikin sanya hannu a kan dokar, da aka yi yau Laraba a fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, gwamnan yaa jaddada ƙudurinsa da kare muradun ma’aikata da kuma tabbatar da jin daɗinsu.
Read Also:
Ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa barin ma’aikatan jihar su kunyata ba, inda ya ce sun kafa tarihi, kasancewar ya sanya hannu a kan dokar ne a ranar da majalisar gudanarwar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta NLC ke gudanar da taronta a jihar, inda shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ya kasance a wurin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamnan ya taka muhimmiyar rawa wajen batun aiwatar da sabon tsarin albashin mafi ƙanƙanta a Najeriya.
Ta ce a lokacin da yawancin gwamnoni ke cewa ba za su iya biyan sabon albashin ba, shi kuwa ya yi tsayin daka kan cewa gwamnoni za su iya.