Kenya ta Koka da Mutuwar ‘Yan Kasarta 89 a Saudiyya

 

Kenya na nazarin hana zuwa neman aiki kasar Saudiyya bayan ‘yan kasarta 89 sun mutu a kasar shekaru biyu da suka gabata.

Jaridar Standard ta Kenya ta ce hukumomin Kenya sun amince da bayanin da Saudiyya ta yi kan dalilin mutuwar ma’aikatan ‘yan Kenya inda Saudiyya ta ce sun mutu ne sakamakon matsalar zuciya.

Amma a cewar jaridar ba a gudanar da bincike kan gawawwakinsu ba domin tabbatar da abin da ya yi sanadin ajalinsu.

Ma’aikatar harakokin wajen Kenya ta ce lamarin na bukatar daukar mataki na yuyuwar hana wa ma’aikata zuwa kasar Saudiyya saboda yawan mace-macen mutanen Kenya.

Kenya ta ce mutum 41 suka mutu a Saudiyya a shekarar nan, yayin da kuma mutum 48 suka mutu a bara kuma yawancinsu ma’aikata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here